A wannan zamani na fasaha, ƙirƙirar app ba shine ƙarshe ba—abinda yafi muhimmanci shine yadda zaka saka app ɗinka a kasuwa domin mutane su sauke shi. Daya daga cikin manyan kasuwanni shine Google Play Store.A wannan post ɗin, zaka koyi yadda ake publishing app ɗinka cikin sauƙi.
1. Buɗe Asusun Developer
Da farko, dole ne ka buɗe account a Google Play Console.
Matakai:
Je zuwa: play.google.com/console
Shiga da Gmail ɗinka
Biya kuɗin rajista ($25 – sau ɗaya ne kawai)
Cika bayananka
2. Shirya App ɗinka
Kafin ka upload app, tabbatar da abubuwa masu zuwa:
✔️ APK ko AAB File
Ana bada shawarar amfani da AAB (Android App Bundle)
✔️ App Icon
Girman: 512x512 px
✔️ Screenshots
Hotunan yadda app ɗinka yake aiki
✔️ Description
Short description (ƙanƙanta)
Full description (cikakke)
3. Ƙirƙiri Sabon App
A cikin Play Console:
Danna Create App
Saka sunan app
Zaɓi:
Free ko Paid
Category (misali: Education, Business, etc.)
4. Upload App
Je zuwa Release > Production
Upload AAB/APK ɗinka
Rubuta release notes (abin da ka sabunta)
5. Cika Store Listing
Wannan shine yadda mutane zasu gani:
Ka saka:
App name
Description
Screenshots
Icon
Feature graphic
6. Saita Content Rating
Google zai tambayeka wasu tambayoyi domin tantance:
Shin app ɗinka yana da violence?
Ko yana da adult content?
Ka amsa gaskiya domin kada a ƙi app ɗinka.
7. Privacy Policy
Dole ne ka samar da privacy policy musamman idan app ɗinka yana:
Tattara bayanan user
Amfani da internet
8. Submit App
Bayan ka gama komai:
Danna Submit for Review
Jira review (yakan ɗauki kwanaki 1–3)
9. Bayan An Amince
Idan Google ya amince:
App ɗinka zai bayyana a Google Play Store
Mutane zasu fara downloading
Muhimman Shawarwari
✔️ Ka guji:
Copy content
Fake apps
Malware
✔️ Ka kula da:
SEO (keywords a description)
App performance
Reviews na users
Kammalawa
Publishing app a Play Store ba abu bane mai wahala idan ka bi matakai da kyau. Wannan dama ce mai girma ga masu developer domin su nuna ƙwarewarsu da samun kuɗi.
0 Comments